Pulse.ng logo
Go

Yadda aka gano gawar janar alkali a Jos bayan watanni da bacewar sa

An gano gawar marigayi Janar Idris Alkali a wata rijiya dake kauyen Gwuchet dake karamar hukumar Jos ta kudu nan jihar Filato ranar Laraba 31 ga watan Oktoba.

  • Published:
Nigerian Army recovers corpse of missing Major-General Alkali play

Major General Idris Alkali (rtd)

(Daily Nigerian)

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa an gano gawar manjo Janar Idris Alkali bayan wata biyu da sanar da bacewar shi.

na gano gawar shi ne a cikin wata rijiya dake kauyen Gwuchet na gundumar Shen dake karamar hukumar Jos ta kudu nan jihar Filato.

Recovered body parts of Major-General Idris Alkali kept in body bag play Gawar marigayin kenan bayan fitar dashi daga rijiyar da aka gano shi (Premium Times/Usman Audu)

 

Kwamandan runduna ta uku ta dakarun kasar kuma shugaban bincike domin gano gawar marigayin, Birgediya Janar Umar Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Laraba 31 ga watan Oktoba.

The shallow grave where Major General Idris Alkali was reportedly buried play Kabarin da aka fara binne marigayin (Channels TV)

 

Janar Mohammed ya ce an samu wannan nasarar ne bisa ga labari da daya daga cikin wadanda suka mika kansu ga yan sanda ya bada.

Janar Mohammed yana mai cewa "Kamar yadda aka sani, mun sanar da bacewar Manjo Janar Idris Alkali ranar 3 ga watan Satumba."

"Saboda haka ne muka bazama nemansa, kuma mun gano motarsa wadda a cikinta muka gano wasu daga cikin kayansa, kuma wannan ne ya bayyana mana cewa wani mummunan abu ya same shi."

"A makon jiya kuma mun gano wani kabarin da aka tone, wanda ya ta tabbatar mana da cewa an kai gawarsa wani wuri bayan an fara binne ta a wurin."

Yace an mika garzaya da gawar sojan asibiti kuma daga nan za'a sanar da jan'izar sa.

Abandoned well in Jos where Major-General Idris Alkali's corpse was found play rijiyar da aka gano gawar Janar Alkali (Premium Times/Usman Audu)

 

Tuni dai rundunar sojoji ta sanar da neman wasu mutum 13 da suke da hujjar cewa da hannunsu wajen bacewar sojan.

Shugaban dakaru masu bincike yace umarni uku aka basu kuma sun cika biyu. Yace sun gano gawar shi da kuma motar shi wadanda sune na daya da na biyu da aka umarce su suyi.

Kamar yadda ya sanar matakin da ya rage shine hukunta duk wadanda ke da hannu a wajen aikata wannan mummunan laifin.

Ya kara da cewa duk wanda aka samu yana da hannu, komai girmansa sai ya fuskanci hukunci.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement