ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna ya bada umarnin a kama malamin da ya yi silar yanke hannayen almajirinsa

Gwamnan ya dauki nauyin kudin maganin yaron kuma yace zai dauki nauyin karatunsa

Makon da ya gabata ne jama'a da dama suka yi Allah-wada gamei da lamarin yaron wanda malaminsa ya janyo masa mummanar lahani a kafafen sada zumunta na zamani.

Hakan ya jawo har mutane da dama suna ta jawo hankalin gwamnatin jihar domin daukan mataki kan lamarin.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na twitter gwamna ya nuna jin dadinsa kan yadda jama'a suka jawo hankalinsa game da yaron mai suna Zubairu da ake zargin Malaminsa ya azabtar da shi har ta kai ga an yanke masa hannaye a asibiti.

Yana mai cewa, "Duk da cewa bana gari amma na baiwa kwamshnan shari'a da harkokin mata da su ziyarci yaron a asibitin da yake jinya. Na kuma baiwa kwamishinan umarnin a kamo wanda ke da alhakin yanke hannaye yaron domin ya fuskanci hukunci".

ADVERTISEMENT

Ya kuma kara da cewa bayan biyan kudin maganin yaron, zai dauki nauyin karatunsa.

Har wa yau dai jama'a na kira na a kawo karshen almajirancin a arewacin Nijeriya domin kawo karshen kalubalen da yara kanana ke fuskanta yayin almajiranci.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT