Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya sallami kwamishnoni 25 daga cikin majalisar sa.

Gwamnan ya umarci tsofaffin kwamishnonin da su mika duk wata dukiyar jihar ga sakaren ma'aikatar su.

Hakan ya tabbata ne a cikin wata takardar sanarwa da shugaban yadda labarai na gidan gwamnatin jihar, Malam Abubakar Shekara, ya fitar ranar laraba 4 ga watan Yuli.

Shugaban ya bayyana cewa sallamar zata baiwa gwamnatin jihar damar sauya tsarin jihar tare da canja tsarin majalisar gwamnatin jihar domin samad da cigaba da al'ummar Sokoto ke bukata.

Hakazalika gamnan yayi ma al'ummar jihar godiya bisa goyon bayan da suka baiwa tsofafin kwamisnonin.

Ga sunayen su kamar haka:

1. Ahmad Aliyu

2. Umar Nagwari Tambuwal

3. Saidu Umar

4. Muhammad Arzika Tureta

5. Muhammad Jabbi Kilgori

6. Abdullahi Maigwandu

7. Surajo Gatawa

8. Abdulkadir Jeli Abubakar III

9. Tukur Alkali

10. Mani Maishinku Katami

11. Muhammad Bello Sifawa

12. Muhammad Bello Abubakar Guiwa

13. Sulaiman Usman SAN

14. Isa Sadiq Achida

15. Aminu Bello Sokoto

16. Bala Kokani

17. Bello Goronyo Esq

18. Manir Muhammad Dan’Iya

19. Kulu Abdullahi

20. Balarabe Shehu Kakale

21. Musa Ausa Gidan Madi

22. Aishatu Madawaki

23. Ahmed Barade Wamakko

24. Garba Yakubu Tsitse

25. Bello Isa Ambarura