ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

PDP tana zargin gwamnan jihar Katsina da yin badakalar biliyan N400

PDP tace duk da kudaden da jihar ta samu har yanzu al'ummar jihare na fama da talauci

Shugaban jam'iyar reshin jihar Alhaji Salisu Majigiri ya sanar da haka yayin da ya gana da manema labarai a garin katsina ranar Talata 2 ga watan janairu.

Shugaban yace wasu manyan jami'an gwamnatin ke amare da kudin jihar wanda hakan ya sanya al'ummar jihar suna fama da talauci tare da shiga yanayin lamuni.

A bisa sanarwar shi, jihar Katsina ta samu biliyan 243 daga asusun gwamnatin tarayya kana ta kara samun biliyan 30 na tallafin kudin Paris amma duk da hakan gwamnati ta ciyo basusukan makuden kudade daga banki.

Majigiri yayi ikirari cewa ajiyar naira biliyan 14.5 tare da wasu kaddarori da gwamnatin PDP tayi a asusu jihar ya sanya jihar take takara da sauran jihohi a matsayin jihar mafi dukiya a kasar.

ADVERTISEMENT

Game da zargin da jagoran PDP yayi shima babban mai yi ma gwamnan jihar Katsina hidima a bangaren watsa labarai Alhaji Abdu Labaran ya mayar da martani inda yake musanta zargi kana yayi kira ga jama'a da suyi watsi da maganar shi.

Alhaji Labaran ya sanar cewa gwamnatin jihar tayi amfani da kudaden wajen gudanar da ingantattun ayyuka wanda zai inganta rayuwar al'ummar jihar.

Daya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin tayi shine gyare gyaren babban asibitin Katsina da Daura da kuma Funtua da Kankiya kamar yadda kakakin gwamnan jihar ya sanar.

Daga karshe kakakin gwamna Aminu Bello Masari yace tuni aka watsi da jam'iyar PDP a jihar inda yake bada misali da ficewar tsohon kakakin majalisar jihar Yau gwajogwajo da kuma tsohon dan majalisar dattawa Ibrahim Ida daga jam"iyar PDP zuwa APC.

ADVERTISEMENT

Ficewar Atiku Abubakar daga jam'iyar APC

Yayin da yake tarbi tsohon kakakin majalisar jihar Yau Gwajogwajo a garin Maiadua, Gwamna Aminu Bello Masar ya kara haske kan ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa daga jam'iyar APC zuwa PDP.

Gwamnan yace babu abun da ficewar shi zata tsinana ma jam'iyar APC. Hakazalika gwamnan yace babu wata fargaba ga jam'iyar game da matakin da tsohon jigon jam'iyar ya dauka domin hakan ba zai hana APC samun nasara a zaben 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT