ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Minista yace ko a gadon jinya, Buhari zai lashe zaben Bauchi, Kano da Sakkwato

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya zanta da manema labaru a wajen kaddamar da jirgin kasan Itakpe-Ajaokuta-Warri ranar juma'a 27 ga watan Yuli.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya zanta da manema labaru a wajen kaddamar da jirgin kasan Itakpe-Ajaokuta-Warri ranar juma'a 27 ga watan Yuli.

Ministan ya mayar da martani ne game da batun sauya sheka da wasu yan majalisar tarayya suka yi daga APC. Yace shugaba Buhari zai samu nasara a jihohin Kano da Bauchi da Sakkwato ko yana saman gadon asibiti yana jinya.

A cikin makon da ya shude ne wasu yan majalisar dokokin tarayya sama da 50 suka sauya sheka daga jam'iyar mai mulki. Sanatoci 15 tare dayan majalisar wakilai 36 suka fice zuwa jam'iyyun adawa.

ADVERTISEMENT

Bayan ga haka wasu gwamnonin APC sun yunkura wajen barin jam'iyar ciki akwai gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom wanda ya fara daukar wannan matakin na barin jam'iyar da ta samar mashi mulki.

Ministan yace ficewar yan majalisar daga jam'iyar APC ba zai tsinana komai ga takarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben badi ba.

Ameachi yace wata kila gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal zai sauya sheka daga APC don cinma manufar sa na zama shugaban kasa.

Yace Gwamnan tare da takwaransa na Kwara tun ba yau ba ake sa ran cewa suna da ra'ayin barin APC. Ya kara da cewa gwamnonin tare da yan majalisar da suka sauya sheka tun asali sun fito ne daga jihohin da shugaba Buhari ke samun nasarar kuri'u.

Ministan ya kalubalanci babban jam'iyar adawa ta PDP inda ya bayyana cewa saura wata shidda da gudanar da zabe amma har yanzu ta gaza fidda gwaninta wanda zai fito takara da Buhari.

ADVERTISEMENT

Ameachi wanda shine shugaban yakin neman zaben Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zuwa nan da yan makonni zasu kaddamar da ayyukan yakin neman kuri'u.

Ya kara da cewa ayyukan da gwamnati ke kaddamarwa a kwana-kwanan nan bata da wata manufa ga siyasa ko zaben 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT