Alummar jihar Gombe sun sadu da wani abun alajabi inda aka haifi wata saniya me kai biyu.

Kamar yadda wani ma'abocin shafin Facebook, Comr Anas Mu'azu ya sanar a shafin sa na dandalin, an haifi saniyar ne a karamar hukumar Billri na jihar.

Daga gani yadda bakin daya daga cikin kawunan saniya ta bude, ba'a iya tantance ko tana raye ko kuma sabanin haka.