Sanannen hamshakin mai kudi, Aliko Dangote, ya fito fili ya bayyana cewa ya shirya yin aure tare da neman tabbatar da burin sa na siyan kungiyar Arsenal.

Dangote wanda yake rike da matsayin bakar fata mafi kudi a duniya kuma na daya a afirka, yayi shekaru da dama bai da mata bayan rabuwar auren sa.

Hirar shi da jaridar Financial Times, Shugaban kamfanin Dangote yace lokaci yayi da zai nemi abokiyar zama domin shekaru na ta tafiya.

" Shekaru ba raguwa suke. shekara 60 ba wasa ba. Lamarin ba zaiyi dadi ba idan na nemi wata alhali banda isashen lokaci. A halin yazu dai akwai ayyukla da dama a gaba na",yace.

Kamar yadda ya bayyana, ayyukan dake gaban shi sun hada da gina matatar man fetur da taki da gina sinadarin mai da iskar ta.

Dangote ya kara da cewa har yanzu bai kawar da burin sa na siyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Yace yana kaunar kungiyar kuma idan ya samu dama zai siye ta.

Yace aikin da yake wajen gina matatar mai ke kawo masa cikas amma muddin ya gama zai dawo da aniyar sa wajen dandalin kwallon kafa.

Haifafen dan jihar Kano yayi aure sau biyu kuma Allah ya albarkace shi da yara uku.