Pulse.ng logo
Go

NEA 2018 Ali Nuhu ya sake fitowa takarar gwarzon shekara

'Sarkin Kannywood' ya fito takarar gwarzon shekara tare da manyan fitattun jaruman Nijeriya a rukunin jagoran shiri na gasar.

  • Published:
AMVCA 2018 play Ali Nuhu ya lashe kyautar bikin bana a rukunin shiri mafi kayatarwa na daga fina-finan hausa (Pulse)

Bayan ya lashe lambar yabo ta gasar AMVCA na bana, fitaccen jarumin fina-finan hausa Ali Nuhu ya sake fitowa takarar gwarzon shekara na gasar Nigerian Entertainment Awards.

'Sarkin Kannywood' ya fito takarar gwarzon shekara tare da manyan fitattun jaruman Nijeriya a rukunin jagoran shiri na gasar.

Zai fafata da jarumai, Femi Adebayo, Blossom Chukwujekwu, Kalu Ikeagwu, Ali Nuhu, Adebayo Salami da Odunlade Adekola wajen lashe lambar yabo.

Ya fito takarar ne bisa rawar da ya taka a cikin shirin 'Mansoor'.

Bikin Nigerian Entertainment awards tana daya daga cikin manyan bukukuwan karrama fitattun jarumi da suka nuna hazaka a dandalin nishadi ta kasa baki daya. Ta sha bambam da sauran domin ana gudanar da bikin ne a wajen Nijeriya.

Bikin na wannan shekarar shine na 13 kuma za'a gudanar da ita ne a birnin Washington DC na kasar Amurka ranar 10 ga watan Nuwamba.

Ga sauran jaruman da suka fito takara a gasar bana kamar haka;

Ali Nuhu ya lashe kyautar AMVCA

Gasar African Magic Viewers Choice Awards wanda aka shirya a birnin Legas ranar asabar 1 ga watan Satumba, shirin MANSOOR ya lashe kyautar shiri mafi kayatarwa.

Shirin ta lashe kyautar sabanin sauran fina-finai da aka hada su takarar na daga cikin fitattun shirye-shirye na rukunin hausa.

A jawabin sa yayin da ya amshi kyautar Ali Nuhu ya mika godiyan sa jaruman mda ma'aikatan da suka taka rawar ganin  wajen shirya shirin MANSOOR.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement