ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

'Sarkin kannywood' ya cika shekara 44 a duniya

Ali Nuhu yana daya daga cikin jagorori dake raya masana'antar Kannywood kuma jakadar arewa ne a sauran masana'antar fim dake kasar har ma da kasashen waje

An haifi jarumin mai tauraro wanda aka yi ma lakabin sarkin Kannywood a garin Maiduguri ranar 15 ga watan Maris na shekara 1974.

Yayi karatun kuruciyar sa a jihar Kano kana ya tafi jami'ar Jos daga baya ya ketara zuwa jami'a birnin Carlifonia inda ta karanci ilimin shirya fim.

Jarumin ya fara harkar fim gadagadan cikin 1999 kuma yana taka rawa wajen shiryawa da bada umarni har ma rubutun shiri.

Ali Nuhu yana daya daga cikin kusoshin Kannywood da suka raya masana'antar bisa gudunmawar da yake badawa wanda bata da iyyaka.

ADVERTISEMENT

Dadewar sa tare da nuna basirar shi na wasan kwaikwayo bai tsaya a kan fina-finan hausa kadai, jarumin yana haskawa a cikin fina-finan kudancin kasar ta Nollywood.

Ya samu kyaututuka da dama bisa rawar da yake takawa a bangaren nishadantarwa cikin gida har da kasashen waje.

Jagoran kamfanin FKD yayi sanadiyar fitowar jarumai da dama da ke tashe a masana'antar a halin yanzu.

Yayi murnar cika shekara 15 da auren uwardakin sa jiya laraba 14 ga watan maris. Sakamakon auren nasu Allah ya albarkace su da yara biyuFatima da Ahmad.

Yau take ranar haihuwar shi, muna masa barka da farin ciki na cika shekara 44 a duniya.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT