Fitaccen jarumi kuma tauraron masanaantar fim ta arewa, Ali Nuhu, ya samu karramawa a wata jamia dake kasar Jamhoriyar Benin.

Jami'ar  ISM Adonai University  dake Porto-Novo babban birnin kasar ta karrama shi da takardar matakin likitan boko kan karatun fannin kasuwanci da kuma samad da cigaba ga matasa.

Bisa ga wannan karamcin da jarumin wanda ke da sarautar 'Sarkin kannywood' ya samu, sunanshi ya samu matsayi inda ya koma Dakta Ali Nuhu.

Tuni dai jarumin ya bayyana farin cikin sa bisa alheri da ya samu a shafin sa na kafafen sada zumunta.

Ali Nuhu ya mika godiyan sa ga ma'aikatan jami'an tare da nuna godiyan sa ga masoyan shi bisa fatan alheri da suka yi masa.