ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dubban manyan yan siyasar Nijeriya sunyi jimamin mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma iyalin marigayi bisa ga rashin da suka samu

Tsohon mataimakin shugaban kasa Dr. Alex Ekwueme ya rasu ne ranar lahadi 19 ga watan nuwamba a wani asibiti dake birnin London bayan rashin lafiya da yake fama da ita.

Dr. Ekwueme shine mataimakin shugaban kasa ta farko da kasar ta samu ta hanyar mulkin dimokradiya. Shine mataimakin shugaba Shehu Shagari zamanin mulkin sa tsakanin 1979 zuwa 1983.

Ya rasu ya rasu yana da shekaru 85 a duniya a asibiti dake birnin London

Bayan sanarwan da dan uwansa Igwe Laz Ekwueme yayi na mutuwar sa, yan kasar sun nuna bakin ciki game da mutuwar sa tare da yi ma iyalen sa ta'aziya ciki har da manyan yan siyasar Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Ga abubuwan da wasu daga cikin su suka yi game da mutuwar sa;

Shugaban kasa Muhammad Buhari

"Nayi jimamin mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Dr Alex Ekwueme. Mutum ne mai kishin kasa kuma mai son ganin hadin kai tsakanin yan kasa da son ganin cigaba a kasa. Sadaukarwan da yayi ya taimaka wajen kafa ginshikin dimokradiya a kasar mu.

"Ina mika ta'aziya ta ga iyalin sa, abokan arziki, gwamnati har ma da jama'ar jihar Anambra, yan kabilar Ibo har ma da sauran yan kasar bisa wanan rashin da suka samu. Ubangiji yaba iyalensa hakurin jure rashin sa.

ADVERTISEMENT

Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari

"Ina cike da kunci da na samu labarin mutuwar dan uwana kuma tsohon mataimakin shugaban kasa. I madadin iyalina ina taya yan Nijeriya jimamin mutuwar sa.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

"A yau ina taya sauran yan Nijeriya jimamin mutuwar daya daga cikin hamshakin yaran kasar Dr Alex Ekwueme. Yayin da kasar ke ta'aziyar mutuwar sa, zamu cigaba da nuna farin ciki bisa ga jajircewan da yayi wajen ganin kasar ta samu cigaba.

Ba zan taba manta da Dr Alex Ekwueme ba bisa ga yanda ya nuna bajintarsa zamanin mulkin mallakar soja. Ubangiji Allah ya ba iyalin sa karfin jure rashin sa.  Dattijon arziki ne kuma adilin shugaba ne, lallai zamu yi kewar sa.

ADVERTISEMENT

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

"Ina cike da takaici da jin labarin mutuwar Alex Ekwueme, tsohon mataimakin shugaban kasa. Mutum ne mai halin kirki.

"Ni da shi mun kasance a cikin yan Nijeriya da suka halarci taron kundin tsarin mulkin na 1995, wanda ya kawo shawarar raba Nijeriya zuwa yankuna shidda. gaskiya zamu yi kewar sa.

Gwamnan jihar sokoto Aminu Tambuwal

"A gare mu al'ummar jihar Sokoto, mutuwar Alex Ekwueme yazo da wani radadi domin shine mataimakin daya daga cikin yaran jihar mu watau Alhaji Shehu Shagari.

ADVERTISEMENT

Marigayi tare da sauran tawagar sa sun iya kokarin su wajen ganin haddin kai, cigaba da zaman lafiya tsakanin yan kasa.

Ita ma jam'iyar APC ta taya sauran yan kasa ta'aziyar mutuwar tsohon dan siyasa kuma mataimakin shugaban kasa n farko da kasar ta samu a mulkin dimokradiya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

If you get these 5 messages on Valentine's Day, you are the side piece

If you get these 5 messages on Valentine's Day, you are the side piece

Valentine's Day: 10 perfect Nigerian songs for the Booless

Valentine's Day: 10 perfect Nigerian songs for the Booless

Valentine's Day: 10 timeless Nigerian love songs you should add to your playlist

Valentine's Day: 10 timeless Nigerian love songs you should add to your playlist

Here are foods to avoid during Lent

Here are foods to avoid during Lent

Top 5 coldest countries in the world

Top 5 coldest countries in the world

6 ways to survive the heat season in Nigeria

6 ways to survive the heat season in Nigeria

5 tips for fasting during the days of Lent

5 tips for fasting during the days of Lent

How to celebrate Valentine's Day when you are in a long-distance relationship

How to celebrate Valentine's Day when you are in a long-distance relationship

AFCON 2023: Should Jose Peseiro stay as Super Eagles boss after final loss?

AFCON 2023: Should Jose Peseiro stay as Super Eagles boss after final loss?

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT