Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta taya wasu mata biyu da suka samu nasara a zaben fidda gwani na takarar kujerun sanata na jam’iyyar APC a jahar Adamawa.

Matan da suka samu wannan gagarumar nasara sun hada da Sanata Binta Garba Masi wanda ke neman zama wakiliyar al’ummar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya da kuma Aishatu Dahiru dake neman darewa kujerar Sanatan jama’a Adamawa ta tsakiya.

Aisha Buhari ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta, Suleiman Haruna ya fitar ranar Talata 9 ga watan Oktoba.

Uwargidan shugaban kasa tana mai sanarwa cewa “Ina addu’ar ganin matan guda biyu da dukkanin sauran matan da suka samu nasarar lashe zaben fidda gwani na samun tikitin tsayawa takara a kakashin jam’iyyar APC su samu nasara a babban zaben 2019".

Tayi kira ga yan takaran da su tsaya tsayin daka wajen cika manufofin jam’iyyar APC, ta yi kira ga yan takarar da su baiwa ayyukan cigaban mata fifiko, tare da samar da tsare tsare da zasu taimaka ma talakawa idan suka samu nasara a zabe mai zuwa.

Sanata Binta Garba Masi ta samu tikitin APC cikin ruwan sanyi bayan rashin samun abokin takara mai neman kujerar.

Ita ma tsohuwar yar majalisar wakilai daga jihar, HajiyaAisha Dahiru, zata nemi zarcewa zuwa zauren majalisar dattawa bayan da ta lashe zaben fidda gwanin da jam'iyar APC tayi.

Yar majalisar wacce aka fi sani da Binani doke maza hudu da suka fito takara da ita wajen zama gwanin APC wacce zata kara a zaben 2019. Ta samu kuri'u 1, 282 yayin da mai binta a baya, Alhaji Wakili Boya, ya samu kuri'u 599 na kuri'un da aka kada.