ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

UNAIDS ta karrama uwargidan shugaban kasa da mukamin jakadanci

Yace uwargidan ta samu wannan matsayin bisa rawar da take takawa wajen bayar da gudummawa ga mata da yara marasa galihu

Wakilin cibiyar na Nijeriya Mista Charles-Martin Jjuuko ya bayyanar da haka a wata takarda da ya fitar ma manema labarai ranar asabar 17 ga wata a garin Abuja.

A sanarwar da ya fitar, za'a mika ma uwargidan shugaban kasa takardar mukamin ranar litinin 19 ga wata a nan babban birnin tarrayya.

Yace uwargidan ta samu wannan matsayin bisa rawar da take takawa wajen bayar da gudummawa ga mata da yara marasa galihu.

Da sabon matsayin Aisha Buhari zata goyi bayan wayar da kan al'umma kan yaduwar cutar kanjamau tsakanin iyaye mata da yaran su da kuma hanyoyin da za'a bi wajen magance yaduwar cutar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT