Pulse.ng logo
Go

Aisha Alhassan Idan baba ya fito takara 2019 ba zan zabe shi

Ministar harkokin mata ta bayyana abun da yasa take goyon bayan Atiku

  • Published:
Aisha ta bayyana dalilin da yasa take goyon bayan Atiku play

Aisha ta bayyana dalilin da yasa take goyon bayan Atiku

Ministar harkokin mata Aisha Alhassan ta bayyana cewa baza ta zabi Buhari indai ya fito takara tare da ubangidan ta Atiku Abubakar.

Ministan ta fadi haka ne a wata hira da tayi da bbchausa ranar laraba 6 ga watan Satumba.

Aisha ta bayyana cewa tun kafin ta shiga siyasa take tare da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar kuma indai ya fito takara shi zata yi wa kamfe.

“Fatan da nayi ma mai girma Atiku nayi shi ne don tun ina aikin gwamnati yake ubandaki na kuma har na shiga shiyasa ya kasance ubandaki na a siyasa sa’anan na biyu baba Buhari bai ce mana zai saya zaben 2019 ba. Ina mai tabbatarwa cewa idan baba zai yi takarar 2019 zanje in durkusa masa ince masa baba na gode da ka bani dama nayi aiki a karkashin ka a matsayin minista amma baba kamar yanda ka sani Atiku ne ubandaki na, indai Atiku yace zai tsaya takara don a yanzu bai ce mana zai tsaya zaben 2019” inji ministan.

Ta kara da  cewa “ abun da yasa nace shine shugaban kasar mu idan Allah ya yarda 2019 shine don muna sa ran zai tsaya takara amma shi da kansa bai ce zai tsaya takara amma indai yace zai tsaya toh abun da na fada a baya zanyi zanje inyi domin in yanzu Atiku yace zai tsaya zabe kuma ina cikin cabinet na baba kuma baba yace zai tsaya na zama munafuka kenan ni kuma ba wanda ya sanni da munafunci ba wanda sanni da butulci kuma ba wanda ya sanni da cin amana. Yanzu ince ba ruwana da Atiku wallahi tallahi ko baba Buhari zaiyi shakka na, zai wannan maciyar amana ce kuma ni bani cin amanar mutane.”

Game da maganganu dake yaduwa na cewa ta fara yin wa Atiku kamfe tun zaben bai maso ba ministan tace tayi maganar ne lokacin da suka kai mashi gaisuwa kuma ba wai tana mai kamfe ba don maganar kamfe bai taso ba.

Tace “ wannan aikin yan adawa ne masu adawa dani. Masu cewa a kore ni minista. Daman ministan ban sa rai zan zama ba Allah ne ya bani”.

Tsohuwar ‘yar takarar gwamna  na jihar Taraba tace Buhari ba zai taba koranta don maganganun da tayi domin shi ba mutum bane irin masu korafi na a korata daga aiki.

A karshe tace Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari mutum ne mai halayya na ƙwarai kuma mutum ne wanda take girmamawa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.