Tsohuwar jarumar fim kuma uawargidan fitaccen jarumi, Mansura Isa tare da tauraruwa Saratu Gidado Daso sun ketara kasa mai tsarki don yin aikin hajji na wannan shekara.

Kamar yadda suka sanar matar gwamnan jihar Kebbi Hajiya Zainab Atiku Bagudu ta dauki nauyin tafiyar su.

Jaruman sun gaza boye farin cikin su na kasancewa cikin wadanda Allah ya nufa zasu gudanar da aikin hajji na wannan shekarar.

A shafin ta na kafar sada zumunta, Mansura Isa ta rubuta "Allah ya saka miki da alheri mummy".

Sun wallafa hotunan su yayimn da suka dirar kasar Saudiya tare da yi ma uwargidan gwamnan godiya bisa halaccin da tayi masu.

Tun a makon da ya shude maniyata daga Nijeriya suka fara tafiya kasar Saudi Arabia don gudanar da aikin hajji na wannan shekara.

Kamar yadda hukumar hajji na kasa ta sanar, kai ga yanzu akalla mahajjata 14,160 aka garzaya dasu kasar.