Sabon shiga  gasar Firimiya na Ingila Fulham tare da sabon abokin adawar ta Huddersfield na neman kawo fitaccen dan wasan Super eagles, Ahmed Musa, don ya taka masu leda a kakar 2018/2019.

Duba da irin rawar da ya taka tare da tawagar Super eagles a gasar kofin duniya na wanan shekara, dan wasa mai tauraro Ahmed Musa ya shiga takardar yan wasa da kungiyar Fulham da Huddersfield na Ingila ke nema.

Ahmed Musa bai samu dama ba a Leicester bisa ga rawar da James Vardy ke takawa wajen zura kwallo a raga wanda dashi masoya da kungiyar ke takama dashi.

Ahmed Musa ya dawo kungiyar Leicester da taka leda a kakar 2016 sai dai amma bai samu damar nuna ma jama'a dabarar sa ba sakamakon rashin samun lokaci da yake fuskanta a kungiyar.

Wata kila idan ya koma Huddersfield ko Fulham tauraron sa zai haska a gasar firimiya na kakar 2018/2019.

Dan wasan dai ya taka rawar gani a gasar kofin duniya wanda ke gudana a kasar Rasha da tawagar Nijeriya. A cikin wasanin rukuni uku da Nijeriya ta buga, dan wasan ya zura kwallo biyu a raga.

Duk da cewa Nijeriya bata yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu, kwallayen da Ahmed Musa ya zura a raga wasan Nijeriya da Iceland yana daga cikin abubuwan da haifar da farin cikin ga yan kasa. Kuma yana daga cikin wanda ya birge a gasar.

Sakamakon kwallo biyu da ya saka a raga a gasar, Ahmed Musa, ya kafa tarihi a tarihin kwallon kafa na Nijeriya. Shine dan wasan tawagar super eagles da yafi kwallo a gasar kofin duniya ta FIFA.