Tauraruwar Kannywood Hafsa Idris ta dauki hankalin jamaa da adon ta.

Jarumar ta wallafa hotunan inda tayi kwalliya mai birgewa. Kamar yadda muka gani jarumar tayi adon ne gagabanin tafiyar ta wani biki da aka gayyace ta.

Hotunan dai sun birge kuma masoyan ta da ma'abotan shafin ta na Instagram sun kasa boye abun dake ran su.