ʼƳan uwa úkku sun láʼanta áddinin kiristanci, sun koma ga addinin Musulunci
An musulunci da "ƴan uwa uku cikin jihar Imo, kuma an shigar da su makarantar Islamiyya a Jihar Kaduna.
Waɗanan ʼƴan uwa, Chinonso, Chika da Chibuzor, sun fito daga ƙauyen Chokoneze a ƙaramin hukumar Mbaise, jihar Imo. Sun yi imani cewa sun ƙarbi musulunci da duka zuciyar su. Wani shafi mai suna "Islam Calling Family" (wato masu kiran iyali su shiga addinin musulunci) akan Facebook, sun yi sanarwa cewa an shigar da waɗannan ʼƴan uwa wani makarantar Islamiyya a jihar Kaduna.
Sun yi sanarwa akan shafin su na Facebook kamar haka:
"Dole ne musulunci tá yadu á ƙasar Ibo."
"A kwanan baya, ʼƴan uwa uku daga uba da uwa ɗaya, sun ƙarbi musulunci a ƙauyen Chokoneze, ƙaramin hukumar Ezinihitte Mbaise, Jihar Imo.”
"Chinonso yá cánja súnán sa zúwá Hassan, Chika ya zama Musa, Chibuzor ya koma Abdulrahman. Mun shigár da su á makarantar Islamiyya cikin jihar Kaduna domin koyon karatun musulunci."
Akwai labarin game da irin wannan canji zuwa ga addinin musulunci a wasu ƙassashen waje, amma babban labari ne a ƙasar Najeriya. Wannan shi ya sa labari na ʼyan uwa ya baza sossai akan yanar gizo da kuma sauran ɗanɗamalin zamantaka.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng