Pulse.ng logo
Go

Adamu Ciroma Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ya rasu

Tsohon ministan kudi kuma jigo na jam'iyar PDP ya rasu yana da shekaru 84 a duniya

  • Published:
Adamu Ciroma, tsohon gwamnan CBN ya rasu play

Marigayi Adamu Ciroma ya rasu yana shekaru 84 a duniya

(Punch)

An samu labarin rasuwar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya kuma tsohon ministan kudi, Adamu Ciroma.

Kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito, marigayin ya rasu a wata asibitin kudi dake garin Abuja bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Tsohon jigon jam'iyar PDP ya rasu ranar alhamis 4 ga watan Yuli kuma yana yana da shekaru 84.

Haifafen dan garin Potiskum dake jihar Yobe, shine gwamnan babban banki tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni na 1977.

Bayan haka ya rike matsaayin ministan kudi karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wa'adi na farko na mulkin sa.

Bugu da kari shine shugaban yakin neman zabe na Obasanjo yayin da tsohon shugaban ke neman zarcewa a zaben 2003.

Gabanin rasuwar sa, marigayin ya taka rawar gani a harkar siyasar kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement