Pulse.ng logo
Go

Barayin shanu Adadin mutanen da suka mutu a jihar Zamfara

Akalla mutum sama da 1300 suka mutu sakamakon hare-haren da yan ta'ada suka kai a jihar na tsawon shekaru 7

  • Published:

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da barayin shanu suka kai a jihar na tsawon shekara 7 ya kai 1320.

Hakazalika an raunata mutum sama da dubu biyu kuma gidaje da gonaki fiye da dubu goma aka lalata a jihar.

Bayanan sun fito yayin da gwamnatin taraya ta tura rundunar sojojin sama jihar domin taimakwa wajen kawo karshen ta'adanci a jihar.

A labarin da BBC ta fitar, sakataren gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Muhammed ya shaida cewa, gwamnati tana cigaba da  bada kudade da sauran kayyakin sassauci ga wadanda lamarin ya shafa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.