Atiku Abubakar ya kai ma tsohon uban gidan sa, Olusegun Obasanjo, ziyara a gidansa dake nan garin Ota na jihar Ogun mdomin neman goyon bayan sa yayin da zaben 2019 ke gabatowa.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar PDP ya isa farfajiyar tsohon shugaban kasa a daidai karfe 1:05 na rana tare da wasu jigan-jigan jam'iyar da ma'aikatan hukumar yakin neman zaben sa.

Hakazalika Atiku ya ziyarci Obasanjo ranar alhamis 11 ga watan oktoba tare da fitattun malaman adini, Bishop Mathew Kukah, da Fasto David Oyedepo da Sheikh Ahmad Gummi.

Wannan shine karo na farko da gwanin PDP a zaben gobe zai kai ma wani ziyara bayan nasarar da yayi na samun tikitin jam'iyar.

Labarin ziyarar tasa ta tada kura inda jama'a da dama suka nuna mamakin faruwar haka duba da dangantakar dake tsakanin sa da tsohon shugaban kasan.

Ga wasu abubuwa 5 masu muhimmanci da Obasanjo ya bayyana masa yayin da suka gana kamar haka:

1. Shugaba mai jiran gado

A farkon jawabin sa, Obasanjo ya kira Atiku a matsayin shugaban kasa gobe.

"Zan fara da taya shugaban-gobe, Atiku Abubakar, murna bisa nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na PDP" inji shi.

2. Yace Atiku ya canza

Obasanjo yace Atiku ya canja matuka wajen inganta kansa sabanin yadda yake kafin suka raba gari.

Yace bayan bincike da nazari tare da duba abubuwan da faru tsakanin su ya gano cewa tsohon mataimakin sa ya ingantar matsayin sa.

3. Ya gafarta ma Atiku

Tsohon shugaban kasa yace ya gafarta ma Atiku inda ya kara da cewa tsohon mataimakin sa ya gane kura-kuran sa.

Yan mai cewa "Kamar yadda na saba bayyanawa, ba abubuwa da kayi mun ne matsalar face abun da kayi ma jam'iya da gwamnatin har ma da kasar baki daya".

"A matsayi na na kirista kuma mai yawan neman gafarar Ubangiji a ko da yaushe bisa ga laifufuka da nake aikata yau da kullum, nayi maka gafara no ko wani laifi da kayi mun kuma ina mai baka shawara da kayi koyi da abubuwan da suka faru a baya kuma ka aiwatar da ayyuka na gari hakika zaka sadu da alheri."

Ya kara da cewa idan akwai wani abu da Atiku yake bukatar sa dayi game da batun a shirye yake don yin haka.

4. Ya bashi shawara

Obasanjo ya kuma shawarci Atiku da yayi aiki da sauran yan takarar da suka fafata tare a zaben fidda gwani yayin yakin neman zabe.

Ya kara da ja masa kunne cewa idan yayi nasarar zama shugaban kasa ya tabbatar da cewa ya bi tsarin kundin tsarin dokar kasa.

5. Atiku shine dan takara mafi cancanta

Duba da kwarewar sa a fannin kasuwanci da harkar shugabanci, Obasanjo yace Atiku shine dan takarar PDP mafi cancanta da zai kayar da shugaba mai saman kujera.

Ya kara da cewa Atiku yana da jama'a a cikin gida da kasashen waje kuma zai samu goyon bayan su.

Daga karshe ya taya shi murna tare da yi masa fatan alheri.