Pulse.ng logo
Go

Labarin cikin hotuna Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi kwana daya bayan dawowan sa daga kasar Togo

Shugaban ya dawo gida Nijeriya daren ranar talata 31 ga watan Yuli. Ga wasu abubuwa da ya yayi washe gari bayan dawowan sa kasar:

  • Published:
Shugaba Buhari a ofishin yakin neman zaben sa da aka gyara play

Shugaba Buhari a ofishin yakin neman zaben sa da aka gyara

(Instagram/buharisallau)

Shugaban kasa Muhhammadu Buhari ya kai ziyarar kwana biyu kasar Togo domin halartar taron kungiyar ECOWAS.

A taron ne kasashen afrika ta yamma suka zabe shi a matsayin sabon jagoran kungiyar.

Shugaban ya dawo gida Nijeriya daren ranar talata 31 ga watan Yuli. Ga wasu abubuwa da ya yayi washe gari bayan dawowan sa kasar:

1 Ya jagorancin zaman majalisar sa

play (Instagram/buharisallau)

Kamar yadda aka saba yi a ko wani ranar laraban ko wani mako, shugaban ya jagoranci zaman majalisar gwamnatin sa a nan babban dakin taro dake fadar sa.

A zaman,  majalisar ta amince da kashe Naira Bilyan 72.9 wajen sake gina hanyar tashar jirgin ruwa na Apapa da ke jihar Legas ind aka baiwa kamfanin Dangote kwangilar aikin hanyar.

Bayan ga haka majalisar ta amince da gyaran tituna dake jihar domin rage cinkoso.

2. Ya karbi bakoncin shugaban kasar Gambia

play (Instagram/buharisallau)

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya kawo ma shugaba Buhari ziyara a nan fadar shugaban dake Abuja.

Shugaban ya shawarci takwaran sa na Gambia kan ya tabbatar da tsara ingantaccen tsarin gudanar da shugabanci domin tabbatar da cigaba a kasar shi.

A nashi jawabin Adama Barow yayi ma shugaban godiya bisa yadda Nijeriya ta taimaka wa kasar shi wajen kafa tsarin dimokradiya a kasar shi. Ya kuma yi shugaban maraba bisa matsayin da ya samu a kungiyar ECOWAS ba zama jagoran ta.

3. Ziyarar gani-da-ido zuwa ofishin yakin neman zaben shi wanda ake gyarawa

play (Instagram/buharisallau)

 

A cikin shirye-shirye da ake yi gabanin zaben 2019, shugaban ya ziyarci babban ofishin yakin neman zaben sa da ake gyarawa a nan garin Abuja.

Shugaban ya nuna farin cikin sa bisa yadda aka canza fuskar ofishin yakin neman zaben sa a zaben 2015. Ofishin dake nan titin Herbert Macauley Way nan unguwar Wuse ya samu halartar man

4. Shugaban ya tattauna da sanatocin APC

Shugaba Buhari ya tattauna da sanatocin APC play

Shugaba Buhari ya tattauna da sanatocin APC

(Instagram/buharisallau)

Wannan shine karo na biyu cikin tsawon sati biyu da shugaban zai gana da yan majalisar dattawa

5. Ganawa da gwamnonin APC

play (Instagram/buharisallau)

 

Ya kuma tattauna da gwamnoni dake karkashin inuwar APC a fadar sa.

Ana san cewa yan siyasan sun tattauna game da yadda za'a gudanar da alamuran jam'iyar duba da yadda wasu daga cikin su suka sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP duk a cikin tsawon mako guda.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement