ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Jam’iyar APC ta janye maganar korar dan majalisa

Jam’iyar APC reshin Kano ta jaddada cewa Abdulmumin Jibrin dan jam’iyar ne mai matukar muhimmanci a cikin jam’iyar kuma zata hukunta duk wadda ke da hannu dangane da korar shi da ake yaɗawa.

Hon. Abdulmumin Jibrin

Jam’iyar APC reshin Kano ta janye maganar korar Abdulmumin Jibrin wadda majalisan wakilai suka dakatar.

Ranar alhamis 15 ga watan juni, shugaban jam’iyar Sani Ranka na karamar hukumar bebeji ya bayyana cewa an kori dan majalisar mai wakiltar kiru/bebeji daga jam’iyar don yana nufin kawo rarrabe cikin jam’iyar.

A sakamakon haka mai magana da yawun jam’iyar reshin kano Bashir Yahaya Karaye ya bayyana ma manema labarai ranar asabar 17 ga watan yuni cewa JIbrin na nan daram-dam-dam a jam’iyar inda yace Jibrin memba ne mai matukar muhimmanci.

Ya kara da cewa wasu daga cikin jam’iyar sun saɓawa yerjejeniya jam’iyar gurin bada bayyani wadda ba daidai. Yace jam’iyar zata dauki matakin na hukunta wadda ke da hannu game da wannan bayyani.

ADVERTISEMENT

“Akwai wata jita-jita da muka samu cewa an kori Abdulmumin Jibrin Kofa, ginshikin jam’iyar a jihar kano da ma kasar baki daya. Wannan labari ya fito daga wasu yan jam’iyar wadda suka sabawa tsarin jam’iyar na bada labari mara gaskiya.”

“Muna kiran jama’a da suyi watsi da wannan magana kuma su san cewa muna hanyar hukunta duk wadda ke da hannu na yada wannan jita-jita.

“Jam’iyar APC bata goyon baya duk wani mai niyar gurɓata yan jam’iyar a wannan lokacin da muke neman biyan alkawulan da muka dauka.”

“Abdulmumin Jibrin yana nan daram dam-dam kuma duk wani taimako da gudumawa da yake badawa don cigaban jam’iyar muna sane dashi.”

A ranar 28 ga watan satumba 2016 majalisar wakilai suka dakatar da dan majalisar bisa ga zargin da yayi ma kakakin yan majalisa da wasu jiga-jigan yan majalisa na canja kasafin kudi

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT