Duk da ayyukan alkhairin da suka gudanar cikin watan  Ramadan gabanin tafiyar su Rasha, Yan wasan Nijeriya Abdullahi Shehu da Ahmed Musa sun kara farantar da ran jamaa da dama sakamakon ziyarar da suka kai Sakkwato da kuma wasan sada zumunta da aka shirya.

Yan wasan sun taka rawar gani a gasar kofin duniya wanda ke cigaba da gudana a halin yanzu duk da  cewa tawagar bata yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Tauraron Ahmed Musa ya haska matuka duba da kwallayen da ya zura a raga wasan Nijeriya da kasar Iceland wasan su na biyu na rukuni a gasar. Gudunmawar da ya bayar ya faranta wa yan kasa rai wanda kai ga yanzu farin cikin bai gama gushe ba.

[No available link text]

Ziyarar zuwa gidan gwamnati da fadar mai martaba

Da farko dai Shehu Abdullahi ya kai ziyara gidan gwamnatin mahaifar sa ta Sakkwato inda gwamna Aminu Tambuwal ya karrama shi da kyututa da dama bisa gudunmawar da yake badawa wajen raya kasa da daga darajar  jihar. Bayan haka ya kuma kai ziyara fadar sarkin musulmi mai martaba Sultan Abubakar Sa'aad na uku.

Dan wasan ya ziyarci fadar sarkin ne tare da abokin sa Ahmed Musa inda suka mika ma jagoran musulman Nijeriya rigar tawagar Super eagles dauke da suna "Sultan".

Mai martaba yayi masu addua tare da yi masu fatan alheri wajen daga darajar kasa da mahaifar su.

Gabanain zuwan su fadar sarkin, yan wasan sun shirya wasa na musamman domin tallafawa gajiyayyu a nan filin sokoto township stadium.

Dandazon al'umar sakwato sun halarci filin domin kallon taurarin yan wasan. An kuma amfani da kudin da aka samu a wasan sada zumunta da aka shirya wajen raya gidauniyar Shehu Abdullahi wanda ke taimakawa marayu da gajiyayyu.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa ya wasan sun kai ziyarar gidan yari inda suka biya kudin fansa ma wasu da ake tsaron su a gidan.

[No available link text]

A sakon da ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta, Shehu Abdullahi yayi da masoya godiya bisa hadin kai da suka bada wajen fitowa a cikin dandazon su domin kallon wasan da suka shirya. Ya kuma yi ma abokin sana'ar shi kuma aminin shi godiya bisa amsa gayyatar shi da yayi.