Babban kotun tarayya dake Kaduna tayi watsi da karar gwamnati kan tsohon shugaban hukumar kwastam Abdullahi Dikko Inde wanda aka kama da motoci 17 na sata

A ranar 20 ga watan febreru 2017 ne huƙumar yaki da rashawa na kasa ta gano motocin a wani ma’ajiya mallakin Dikko a titin Nnamdi Azikiwe dake jihar Kaduna.

Sun gudanar da bincike a ma’ajiyar bayan sun samu labari cewa akwai wasu duƙiyoyin sata a ma’ajiyar

Mai shari’a S.M.Shuaibu ya hukunci na a ƙaddamar da motocin ma gwamnatin tarayya ranar 24 ga watan febreru.