Ga wasu muhimman labarai da suka fita a makon da ya gabata cikin Nijeriya.

Jaruma Mansura Isa ta raya ranar samun yanci da wasu kayatattun hotuna

Tsohuwar jaruma kuma uwargidan shahararren jarumin Kannywood, Mansura Isa,  ta fitar da wasu zafafan hotuna na raya zagayowar ranar samun yancin Nijeriya.

Shugaban gidauniyar Todays life foundation ta taya kasar murnar cika shekara 58 da samun yancin zama kasa mai zaman kanta.

Tauraruwar ta wallafa hotunan masu jan hankali a shafin ta na kafafen sada zumunta tare da taya kasar murnar zagayowar wannan muhimmin rana.

Ganduje ya samu tikitin APC, zai kara da surukin kwankwaso da yan takarar sauran jam'iyu

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya lashe zaben APC na neman zarcewa a saman kujerar da yake kai. Ya lashe zaben jam'iyar da kuri'u mafi rinjaye.

A bangaren PDP kuwa, dan takarar Kwankwaso yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na PDP.

Abba K. Yusuf ya doke tsohon mataimakin gwamnan Kano, Farfesa Hafeez Abubakar da Salihu Sagir Takai wajen zama gwanin PDP a zaben 2019 dake gabatowa.

Ya samu kuri'u 4000 yayin da Takai ya samu 307 sai kuma farfesa Hafiz wanda ya samu kuri'u 70.

An soke zaman majalisa na mako-mako

A cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Femi Adeshina, ya fitar zaman majalisar gwamnatin tarayya ba zata gudana wannan makon bisa ga wasu dalilai na siyasa.

Sanarwar tace an dakatar da zaman ne bisa ga ayyukan siyasa da ake fama da shi a kasar a halin yanzu musamman zaben fidda da gwani na jam'iyun kasar.

Kamar yadda sanarwar tace mafi yawancin yan majalisar suna cikin masu gudanar da wadannan zabunan a jihohin daban-daban don haka aka dakatar da zaman wannan makon domin basu damar mayar da hankali wajen zaben.

Gwamnan jihar Legas ya gaza samun tikitin APC na sake tsayawa takara

Gwamna Akinwunmi Ambode ya sha kashi yayin da jam'iyar APC ta jihar Legas ta kaddamar da Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda da gwani da aka gudanar a jihar ranar Talata 2 ga watan Octoba.

Jam'iyar ta kaddamar da sakamakon zaben duk da cewa kwamitin dake sa ido ga zaben jihar da uwar jam'iyar ta tura jihar ta soke zaben.

Shugaban jam'iyar APC na jihar Legas, Tunde Balogun, ya sanar da sakamakon zaben tare da kawar da labarin soke zaben da kwamitin uwar jam'iyar tayi.

A sanarwar da ya fitar, Sanwo- Olu ya dankari gwamna mai saman kujera da kuri'u mafi rinjaye.

Babajide Sanwo-Olu ya samu kuri'u 970, 851 yayin da gwamna Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72, 901 cikin kuri'u sama da miliyan daya da aka kada.

Ado Gwanja zai angwance kwanan-nan

Mawakin zai angwance ga amaryar shi, Maimunat Kabir Hassan Danauta, cikin wannan wata.

Za'a daura auren su ranar 12 ga watan Oktoba a jihar Kano dai dai karfe hudu na yamma.

Jarumin wanda ake ma lakabi da 'Limamin mata' ya wallafa katin gayyata na auren shi a shafin sa. Hakan ya biyo bayan hotunan kafin-aure da ya fitar.

Ministan Buhari ta doke danta wajen zama gwanin APC a jihar Yobe

Karamar ministan harkokin kasashen waje, Hajiya Khadija Ibrahim, ta doke dan abokiyar zaman auren ta wajen zama gwanin APC na takarar wanda zai wakilci dundumar Damaturu/Gulani/Gujba/Tarmuwa a majalisar wakilai na tarayya.

Hajiya Khadijah Bukar Abba Ibrahim

Baturen zaben fidda gwani da jam'iyar APC ta gudanar a jihar, Farfesa Abba Gambo, ya kaddamar da ita a matsayin wacce ta lashe zaben takarar kujerar ranar Laraba 3 ga watan Oktoba.

A zaben aka gudanar, Hajiya Khadija ta samu kuri'u mafi rinjaye inda ta samu 1295 yayin da shi kuma danta, Muhammed Ibrahim, ya samu kuri'u 15.

Jimi Agbaje zai sake karawa da dan takarar APC wajen zama gwamnan Legas karkashin jam'iyar PDP

Jimi Agbaje shine wanda yayi nasarar zama gwanin jam'iyar a zaben cikin gida aka gudanar ranar juma'a 5 ga watan Oktoba.

Ya doke abokin takarar shi, Deji Doherty, na zama gwanin jam'iyar bayan da ya samu kuri'u 1,100 yayin da shi kuma Doherty ya samu 742.

Gwamna Bindow ya doke kanin uwargidan shugaban kasa da Nuhu Ribadu wajen samun tikitin APC na takarar Gwamna

Gwamnan jihar Adamawa, Muhammed Jibrilla Bindow ya doke kanin uwargidan shugaban kasa, Halilu Ahmed da kuma tsohon shugaban hukumar EFFC, Nuhu Ribadu, wajen zama dan takarar APC a zaben 2019.

Shugaban kwamitin zaben jihar Adamawa na jam'iyar, Ahmed Jibrin ya sanar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

Shugaban ya sanar da haka ne a safiyar ranar Lahadi 7 ga watan Oktoba inda yace gwamnan ya samu kuri'u 193,656 yayin da sauran abokan takarar sa suka samu 15,738  da  8,364.