Yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, mutane da dama sun mutu

Maharan sun sake kai hari yayin da al'ummar jihar ke ganin cewa an tsawaita tsaro domin kawon karshen yan bindiga da suka addabi jama'a

Kakakin hukumar  DSP Mohammed Shehu ya bayyana ma NANA cewa maharan sun kai harin ne a safiyar ranar laraba kuma tayi sanadiyar mutuwar mutum uku da raunata mutane da dama.

Shehu yace maharan sun bude wuta inda suke ta harbe-harbe ba da sanin al'umar garin.

Yace al'umar garin cikin gaggawa suka sanar da jami'an tsaro wanda sanadiyar hakan an samu nasara wajen katse harbin da suke.

Kakakin ya kuma sanar cewa jami'an hukumar sunyi nasarar korar maharan kuma sun raunata wasu daga cikin su sakamakon musayyar wuta da suka yi.

Daga karshe kakakin yayi kira ga al'ummar garin da su sanar da jami'an tsaro muddin sun ci karo da wanda yaji rauni sakamakon harbin bindiga ko kuma yana mai neman magani.

Rahoton BBC kan harin

A wata rahoton da BBC ta fitar, wani ganau ya shaida wa wakilin ta cewa yan bindigar sun kashe mutum 13 a harin farko da suka kai ranar talata.

Ya kara da cewa yan bindigar sun sake komawa washegarin ranar laraba inda suka bude wuta yayin da ake jana'izar wadanda aka kashe ranar takata din.

Sakamkon harin na biyu da suka kai mutum biyu sun rasu kuma wasu da dama ba'a gan su ba.

Ta'adancin yan bindiga a jihar

An dade ana fama da kashe-kashen mutane a jihar Zamfara, al'amarin dai har yanzu an kasa kawo karshen ta duk da ikirarin da jami'an tsaro keyi na tabbatar da tsaro a jihar.

Wannan sabon harin yazo ne yayin da al'ummar jihar ke tunanin dawowar zaman lafiya sakamakon kashe gawurtaccen dan bindiga wanda ake kira "Buharin Daji".

Ziyarar jaje da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar sakamakon illar da hare-haren da yan bidigar suka kai kwanan baya, shugaban yayi albishir na tsawaita tsaro inda yake cewa gwamnatin sa za ta inganta yanayin aikin jami'an tsaron da aka girke a jihar Zamfara don ba su karfin gwiwar kawo karshen 'yan ta'addan da suka addabi yankunan jihar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Top 10 happiest countries in Africa in 2022

Top 10 happiest countries in Africa in 2022

9 most expensive African countries to rent a one bedroom apartment, based on property price to income ratio

9 most expensive African countries to rent a one bedroom apartment, based on property price to income ratio

These 6 countries have the highest unemployment rates in Africa

These 6 countries have the highest unemployment rates in Africa

Here are the top 10 cities in Africa where the most rich people live

Here are the top 10 cities in Africa where the most rich people live

'Funke and my dad cheated on each other' - Funke Akindele's stepson continues to drag her on Instagram

'Funke and my dad cheated on each other' - Funke Akindele's stepson continues to drag her on Instagram

Here are the top 10 African countries that smoke the most cannabis

Here are the top 10 African countries that smoke the most cannabis

Blossom Chukwujekwu's ex-wife Maureen Esisi reacts as he remarries

Blossom Chukwujekwu's ex-wife Maureen Esisi reacts as he remarries

5 films you should have seen as a die-hard Nollywood fan

5 films you should have seen as a die-hard Nollywood fan

Okada ban: Chaos as Lagos task force impounds 200 motorcycles in Ojo

Okada ban: Chaos as Lagos task force impounds 200 motorcycles in Ojo