Akalla mutum talatin da biyar (35) suka rasu sakamakon gobarar da iskar gas ya haddasa a wani gidan mai dake garin Lafia na jihar Nasarawa.

Lamarin ya faru ne ranar litinin 10 ga wata da misali karfe 10 na safe bayan iskar gas ta malalo daga gidan man Natson har zuwa ga wani babur dake kusa.

Gobarar ta kona motocin da ke ajiye a bakin hanya da kuma masu wucewa, da kuma kona shaguna da dama.

Mutanen da gobarar ta rutsa dasu sun samu munanan kuna.

Kamar yadda shaidu suka sanar tuni aka ruga da wadanda gobarar ta ratsa dasu asibitin Dalhatu Araf Specialist Hospital dake nan garin.

A labarin da jaridar The Nation ta fitar gwamnatin jihar ta bada umarni na a mayar da masu jinyar babban asibitin tarayya dake Keffi domin cigaba da samun magana.