Dan takarar gwamnan Katsina karkashin inuwar PDP a zaben 2015, Injiniya Musa Nashuni, ya sauya sheka zuwa jamiya mai mulki ta APC.

Sabon sanatan yankin Daura, Ahmed Babba-Kaita, ya tarbe shi zuwa APC ranar Laraba 3 ga watan Oktoba a karamar hukumar Kankiya.

Nashuni yace babban dalilin da ya sa ya shigo inuwar APC shine duba da irin shugabanci nagari da jam'iyar ke aiwatarwa karkashin jagoranci gwamna Aminu Bello Masari.

Yayi ikirari cewa shi da dinbim magoya bayan sa zasu iya bakin kokarin su wajen ganin APC tayi nasara a zaben 2019.

A jawabin sa wajen tarban tsohon dan takarar, Sanata Ahmed Kaita ya jinjina masa bisa matakin da ya dauka na shigowa APC tare da magoya bayan sa.

Yayi kira ga sauran ya'yan jam'iya da su bashi hadin kai wajen ganin jam'iyar ta cinma manufar ta na samad da nagartaccen shugabanci a jihar Katsina.

Injiniya Musa Nashuni ya fito takarar Gwamna da gwamna mai saman gado a zaben 2015.

Ya kara fitowa takara gabanin zaben 2019 karkashin jam'iyar adawa ta PDP sai dai amma bai yi nasarar zama gwanin jam'iyar.

Ya fice daga jam'iyar bayan da PDP ta sanar da Yakubu Lado a matsayin wanda zai fito takarar gwamna a zaben 2019.