Kwamishnan shariá na jihar Alhaji Ahmad El-Marzuq ya fitar da wannan kashedi a wata hira da yayi da wakilin NAN a garin Daura ranar litinin.
Gwamnati tayi wa matasa gargadi kan amfani da duniyar gizo wajen cin fuskar magabatan su
Kwamishnan yace kafafen sada zumunta hanya ce ta bunkasa cigaba ba akasin haka ba.
Ya sifanta yadda matasa ke amfani da kafafen sada zumunci wajen cin fuskar magabatan su a matsayi abun takaici.
El-Marzuq ya jaddada cewa zage-zage da kalamun batanci ya kan haifar da sabani da rashin zaman lafiya tsakanin mutane kuma addini ya umarci duniya da ta rungumi kyakyawan hali kuma ayi watsi da mummunar hali.
Babban alkalin jihar Katsina ya sanar cewa hukuma dokoki na kasa ta shirya hukunta duk wani abun da ya haifar da kalamun batanci ko zage zage don haka duk masu aikata hakan suyi watsi da ire-iren dabiu'n.
Ya jinjina wa gwamnatin gwamna Aminu Bello Masari wajen bunkasa harkar shari'a jihar kana yayi kira ga al'ummar jihar da su cigaba da goyon bayan gwamnati wajen samad da ingantaccen cigaba a duk fadin jihar ba tare da yin la'akari da bambamcin jam'iya.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng