ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

wani janar na sojoji ya samu raguwar matsayi don ya siyar da filin jami’an tsaro

An bukaci shi da ya mayar da miliyan N23 wanda shine ƙimanin kudin filin da ya siyar ma kanshi

An kama shi da laifin magudi

Kotun shari’a ta sojoji ta rage matsayin wani manjo janar Ibrahim Sani zuwa birgediya janar bayan an kama shi da siyar da filin sojoji.

Kotun ta hukunta tsohon shugaban fannin kirkira ta sojoji a ranar alhamis 20 ga watan Yuli

Shugaban kotun AVM James Gbum ya rage matsayin bayan kotu ta kama shi laifufuka da suka danganci maguɗi.

A zaman da aka yi a kotu dake barikin mogadishu na Asokoro, shugaban kotun ya umurci wanda ake zargi da ya mayar da miliyan N23 wanda shine kudin da ya samu bayan ya siyar da wani sashen filin ma kansa.

ADVERTISEMENT

Shugaban kotun yace game da  hukuncin dauri sai an samu tabbacin yin haka daga majalisar sojoji na kasa kana za’a zartar da haka.

Babban alkalin Sani mista Paul Sule yace zasu roki majalisar da ta yi watsi da hukuncin.

Sule ya kara da cewa idan majalisar sojoji bata yi watsi da hukuncin zasu kai kukan su zuwa kotun ɗaukaka kara na kasa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT