ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wike ya nace, ‘mallakin gwamnatin jihar Rivers ne’

Gwamnan yana iƙirari cewa kudin mallakin asusun jihar Rivers ne

EFCC staff sweating while counting discovered cash in an Ikoyi apartment

Gwamnar jihar Rivers Nyesom Wike yayi iƙirari cewa kudin sata da aka gano a birnin ikoyi

Yayi wannn iƙirarin a wani shiri da gidan talebijin Channels TV suka shirya. Yace gwamnatin shi na jiran gayyatar hukumar da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada na yin bincike don gano hakikanin wadda ke da kudin.

Hukumar yaƙi da rashawa sun gano kudin a wani gida dake osborne tower cikin birnin ikoyi dake jihar lagos.

Wike yana iƙirari cewa kudin na jihar Rivers ne wadda tsohon gwamnan jihar Rotimi Ameachi ya saci sanda yake mulki.

ADVERTISEMENT

Yace yana jiran hukumar bincike wadda Mukaddashi shugaban kasa ke jagoranta don “sun san abun da suke yi’ kuma ya kamata aji kukar su dangane ga iƙirarin da suke yi.

Ranar talata 6 ga watan yuni, mai shari’a Sule Hassan ya bada umarni na  kaddamar da kudin ma gwamnatin tarayya. Jin haka Wike yace, “wannan ba zai yiwu ba, umarnin da aka bayar na wasa ne’

“Ko suna so ko basu so zan kara fadi, a fito da rahoton binciken da aka yi na gano hakikanin wanda ke da kudin mu gani. Daga nan zasu san matakin da zamu dauka”

“Muna da hujja na nuna cewa kudin mallakin gwamnatin jihar Rivers ne”

“Basu son a tona asiri su don kada gwamnatin taji kunya ko kuma jam’iyar su taji kunya”

ADVERTISEMENT

“In ba haka mai ke hana su fitar da rahoton?”

Zargin da Wike yayi ma Ameachi ya haifar da halin mage da kare tsakanin shi da Ministan sufuri.

A da ana zargin mutane da dama da mallakar wannan kudin, ciki akwai hukumar National Intelligence Agency (NIA) , tsohon shugaban jam’iyar PDP Adamu Muazu, sanata Solomon Deola mai wakiltar jihar lagos maso yamma da kuma tsohuwar direkta na hukumar farashi da siyar da samfurin man fetur Esther Nnamdi-Obue.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT