Bayan wasan ta da kasar Iceland wanda aka tashi 2-0, yan Nijeriya sun kasa boye farin ciki dake tattare dasu sakamakon wasan cikin su har da Adam Zango.

Nijeriya dai ta lallasa abokan adawar ta wasan ta na biyu a gasar kofin duniya kuma Ahmed Musa shine jarumi wanda ya ceci kasar bayan ya zura kwallaye biyu a wasan.

Yan Nijeriya dai kai ga yanzu suna cigaba da murna yayin sakamakon wasan ya zama abun muhawara a kafafen sada zumunta da kafofin watsa labarai.

Jarumin ya wallafa faifan bidiyon a shafin sa na Instagram bayan jerin sakonin da ya fitar na taya murna.

Kamar yadda za'a gani a bidiyon jarumin yana kwaikwayan rawar Shaku-shaku wanda mamaye ko wace rawa a Nijeriya halin yanzu.