ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Karuwai da 'yan kwaya na mun kallon ban girma - inji Hauwa Waraka

Jaruman ta shaida cewa yawan fitowar da take a matsayin karuwa ko yar banza a fim ba zabin ta bane

Fittaciyar jaruma fim Hauwa waraka ta bayyana cewa karuwai da yan kwaya na girmama ta idan suka ci karo da ita.

A wata hirar ta mussamman da tayi da bbchausa, tauraruwar fim ta shaida cewa yawon fitowar ta a fim a matsayin karuwa ko yar banza ba zabin ta bane.

A bayanin ta duk wani shiri da mai bada umurni ya bata take yi kuma a matsayin ta na yar sana’ar fim dole ta aiwatar da haka, ita dai ta sanar cewa ko sigari bata sha kuma tana ma duk masu aikata haka addua na Allah ya shirye su.

Jaruma Hauwa ta fada cewa wasu daga cikin karuwai da yan kwaya na girmama ta idan su ka ci karo da ita don suna kallon ta a matsayin “oga” a harkar.

ADVERTISEMENT

Game da zargin da ake ma yan fim na yin madugo da luwadi da sauran ayyukan banza tayi kira ga masu kallon su da haka da su daina kuma su dinga kallon su da daraja.

Ta kara da cewa duk masu yada zargin idan aka tsare su baza su iya kawo shaidar zargin da suke ma yan fim kuma dole a samu fata-gari a ko wani masana’anta amma tunda basu gani da idon su ba toh su daina masu kallon haka kuma a dinga masu kyakyawar fahimta.

A karshe ta shaida cewa bata da aure amma tana sa ran cewa nan gaba zata yi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT