Shugaban kungiyar Emeka Rollas ya rantsar dashi ranar lahadi 25 ga wata yayin da suka kai ziyarar girmamawa arewa.
Shima babban jarumi kuma shugaban kungiyar masu shirya fina-finai a arewa Abdullahi Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Baba Karami ya samu karramawa inda aka nada shi a matsayin shugaban kungiyar reshin jihar Kano.
Manyan jaruman Kannywood da suka halarci bikin kaddamarwa sun hada da Sani Danja da Umar Gombe da manyan masu ruwa da tsaki a kungiyar daga arewa da sauran yankuna na kasa.