A labarin da Daily Post ta fitar, wani kwakkwarar majiyi ya sanar masu cewa yan ta'addar sun kasa yan matan zuwa kashi biyu.
Bangare daya suna nan jihar Borno inda dayen bangaren an katare dasu zuwa wata kauye dake kasar Nijar.
Kamar yadda labarin ya fito, majiyin ya shaida cewa "An sallake dasu ne ta hanyar kwale-kwale kuma a yanzu suna nan garin Duro wanda take iyakar jumhoriyar nijar da Nijeriya".
"Suma dayan bangaren sun ware zuwa garin dake karamar hukumar nan jihar Borno" ya kara.
Bangarori na kungiyar Boko haram
Jaridar ta kara fitar cewa tawagar Musab Albarnawi na daga cikin boko haram suka yi awon gaba da yan matan.
Tawagar dai tana da alaka da kungiyar ISIS kuma sun fiye safara tsakanin iyakar kasar Chad da jumhoriyar Nijar.
Kungiyar Boko kamar yadda labari ya fito sun rabu zuwa kashi biyu kuma bangaren Abubakar Shekau suka sace yan matan garin Chibok.