Shugaban ya ki amince da wannan kudirin sakamakon wasikar da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya tura masa ranar talata 27 ga wata domin ya sa hannu.
Shugaban yace dalilin da ya sanya bai sanya hannu ga kudirin shine rashin arzikin wajen tafiyar da alamuran hukumar idan aka kafa ta.
Bayan rahoton da wata kwamiti ta musamman da aka kafa domin lura da alamuran da ya danganci sharia da hakkin dan Adam, majalisar dattawa ta fitar da kudirin kafa wannan hukumar.
Dan majalisar mai wakiltar jihar Gombe Bayero Nafada ya gabatar da wannan kudirin ga zauren yan majalisar domin samun goyon baya a ranar 25 ga watan Yuli na 2017.