Pulse logo
Pulse Region

Sarkin Kano ya samu sabon matsayi daga gwamnatin jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya kaddamar ya da kwamitin zuba jari da tattalin arziki tare da kwamiti ta musamman kan hawan Durbar da ake gudanarwa ko wace shekara a jihar.

A taron kaddamarwa da ya faru a zauren fadar gwamnatin jihar Kano, gwamnan yana mai alfahari cewa wannan sabbin kwamiti biyu da aka kaddamar zasu taimaka wajen raya jihar tare da jawo masu kudi da dama wajen zuba jari a jihar domin cinma burin samad da ayyukan cigaba a jihar.

Kwamitin hawan durbar da aka kaddamar wanda kwamishnan kasuwanci Alhaji Ahmed Rabiu ke jagoranta zata wayar da kan al'umma tare da shirya ayyukan bunkasa tarihi ta hanyar hawan da ake shiryawa ko wace shekara.

A jawabin sa wajen taron kaddamarwa sarkin Kano ya yi ma gwamnan jihar Kano bisa wannan kokarin da tayi na kafa kwamitin domin raya jihar Kano.

Subscribe to receive daily news updates.

Next Article