Pulse logo
Pulse Region

PDP ta samu dan takarar da zai fafata da na APC a zaben 2019

Jimi Agbaje
Jimi Agbaje

Babban jamiyar adawa ta PDP ta samu dan takara da zai fafata da yan takarar sauran jamiyu a zaben gwamnan jihar Legas na 2019.

Jimi Agbaje shine wanda yayi nasarar zama gwanin jam'iyar a zaben cikin gida aka gudanar ranar juma'a 5 ga watan Oktoba.

Ya doke abokin takarar shi, Deji Doherty, na zama gwanin jam'iyar bayan da ya samu kuri'u 1,100 yayin da shi kuma Doherty ya samu 742.

Agbaje shine gwanin jam'iyar a zaben 2015 kuma ya fito takara da gwamnan jihar Legas  na yanzu a zaben sai dai bai yi nasarar lashe zaben ba.

Akinwunmi Ambode yayi nasara a zaben inda ya samu kuri'u 150,000 sama da wanda aka kada ma Agbaje.

Dan takarar PDP zai kara da gwanin APC, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya doke gwamna mai barin gado wajen zama jagoran jam'iya mai mulki a zaben 2019.

Subscribe to receive daily news updates.

Next Article