Jami'an tsaron sun samu nasarar kubitar dasu a daidai garin Jalli-Muwarta dake iyakar jihar Yobe da Borno.
Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da wannan babban nasarar da rundunar sojoji suka yi yammacin ranar laraba 21 ga wata
Kamar yadda majiya suka ruwaito yanzu haka an tafi da yan matan asibiti dake karamar hukumar Gaidam domin duba lafiyar su kana a zarce dasu Damaturu babban birnin jihar Yobe.
Yan ta'adar sun saci yan matan ne a ranar litinin da ya gabata yayin da suka kai harin garin Dapchi.