Dakarun 1 Division na rundunar sojojin Nijeriya sunyi fata-fata da wasu yan bindiga tare da kama wani barawo mai satar mutane a yankin kananan hukumomin Chikun da Birnin gwari na jihar Kaduna.

Mataimakin kakakin rundunar sojojin kasa Kanal Mohammed Dole ya sanar da haka yayin da ya zanta da manema labarai a garin Kaduna.

Yace an samu wannan nasarar ne sakamakon sintirin da dakarun WHIRL PUNCH na rundunar suke yi domin tabbatar da zaman lafiya tare da kawo karshen aika-aikar yan fashi da makami da suka addabi al'ummar yankin Birnin-gwari da hanyar Abuja zuwa jihar Kaduna.

Kakakin ya kara da cewa dakarun sunyi fata-fata da wasu yan bidigar guda shida a kauyukan Kidandan da Unguwan Bilya da Sofa da Unguwan Nakuli na karamar hukumar Birnin gwari ranar 10 ga watan Satumba.

Sun kuma kai hari kauyukan Kidan Isa da Gidan Haruna da Mobale da Kuduru inda suka fatattaki yan bidiga hudu yayin da wasu daga cikin su suka tsere da raunuka daga harbin bindiga.

Cikin makaman da sojojin suka gano a hannun yan fashi akwai kunshin harsashin bindigar AK-47 da Albarusai da bindigar gargajiya tare da wayoyin salula guda biyu.

Mutumin da aka kama mai suna Musa, ana zargi shine ya sace wani Alhaji Ahmadu tare da wasu guda biyu a jihar Kano.

Daga karshe Muhammed Dole yayi kira ga jama'a da su taimaka da cigaba da labari cikin lokaci da zai taimaki jami'an tsaro wajen cinma manufar su na tabbatar da tsaro.