ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ziyarar ta'aziya muka kai ma shugaban kasa, ba ta siyasa ba

Hirar shi da manema labarai NAN bayan ganawar da suka yi da shugaban Bisi Akande ya musanta wannan zargi inda ya bayyana cewa sun zo ne domin mika ta'aziya da nuna jaje ga shugaban sakamakon rasuwar yan uwan shi biyu.

Ranar 13 ga wata ne jiga-jigan suka ziyarci fadar shugaban kasa wanda yasa wasu ke ikirari cewa harkar siyasa ce ta kai su wajen shugaban.

Jigon jam'iya mai mulki ya soki PDP inda ya zargi ta da yadda jita-jitan karya game da zuwan su fadar shugaban kasa tare da yin ikirarin cewa babu abun alfahari da suka tsinana zaman su a karagar mulkin kasa na tsawon shekaru 16.

Daga karshen Bisi Akande ya jaddada cewa jam'iyar su tana tare da nasara ganin yadda jiga-jigan dake cikin ta ke iya bakin kokari wajen samad da haka. Ya bayyana hakan tare da bada misali da kwamitin da shugaban ya kafa na neman sulhu a jam'iyar wanda aka nada Bola Tinubu a matsayin jagoran tafiya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasa yan uwansa biyu. Aisha Mamman wanda take matar dan uwan shi da kuma Halima Dauda diyar dan uwanshi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT