ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan majalisa ya tada kura, ana shirin ladabtar dashi

Dan majalisar ya fasa kwai inda ya bayyana adadin kudin da yanbmajalisar ke amsa ko wani wata bayan albashi

Hirar shi da jaridar TheNews, dan majalisar ya bayyana cewa yan majalisar suna amsarN13.5M ko wani wata bayan  N750,000 da suke karba a matsayin albashi.

Ya kuma bayyana cewa suna samun naira miliyan 200 domin gudanar da ayyukan cigaba a mazabar da suke wakilta.

" Za a gaya maka cewa akwai wasu kudade ajiye domin ayyukan mazabar ka. Kai ne zaka je ka fadi musu abinda za kayi wa mutanen ka, daga nan sai ma’aikatan da ke rike da kudin ta yi maka aikin. Sai dai lamarin akwai badakala a cikin ta"  yace.

Wannan lamarin ya jawo tsaiko inda abokan aikin sa na zauren maalisar sun bayyana facin ran su game da lamarin.

ADVERTISEMENT

Tun ba yau ba ake fafatawa da yan majalisar kan bayyana adadin kudin da suke karba ko wani wata sai gashi arha Shehu Sani ya fallasa ga kunnen jama'a.

Wasu daga cikin yan majalisar wadanda suka boyewa suna sun bayyana ma premiumtimes cewa bayanin da Shehu Sani ya fitar zai janyo abun aibi ga yan majalisar kuma zai haifar da rarrabuwar kai tsakanin su.

Matakin ladabtarwa

Hakazalika wasu daga cikin yan majalisar dattawa da na wakilai sun zage damtse wajen ladabtar da shi kan batun.

An samu labari cewa yan majalisar ya shirin tunzura shugaban majalisar Bukola Saraki kan hana shi halartar taro na musamman tsakanin su musamman idan zasu tattauna kan batun kudi.

ADVERTISEMENT

Akwai kuma kishinkishin tuhumar dan majalisar ga kwamitin ladabtarwa na majalisar.

Idan kwamitin ta kama shi da laifi Shehu Sani yana iya fuskantar dakatarwa na tsawon watanni 6 zuwa 12.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT