ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ko dai Yaran North Side sun watse ne?

An kwana biyu da jin wakar su tare ko me ya jawo haka?

Hakika mun kwana biyu da jin wakokin shahararren mawakan hausa hip-hop wato Yaran North Side.

Yaran North Side mawaka ne yan gida daya kuma Faruk Abdullahi wanda aka fi sani da likitre ke jagorantar su.

Fitattun mawakan wadanda suka shahara a Arewacin ƙasar cikin tawagar su akwai Dj Abba da Teeswag da Jigsawmujee da Geeboy tare da Feezy.

YNS kamar yadda ake kiran su sun dade suna nishadantar da yan arewa da salon wakokin su ta hausa hip hop kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen fitar da wakoki cikin harshen hausa domin bunkasa al'adar yan arewa.

ADVERTISEMENT

Mawakan Wakar 'Wabab' da 'Su baba ne' da sauran wakoki da ya zagaye ko wani lungu da saƙon biranai jihohin arewa har ma da sauran yankunan dake ƙasar.

Su baba ne kamar yadda ake kiran su sun kasance tamkar muryar matasan arewa a fanin waka.

Bayan wakokin su da suka yi tare shekaru baya jita-jita nata yaduwa cewa mawakan sun sa zare tsakanin su domin wasu daga cikin su na ganin cewa basu samu damar nuna basirar su ga bainar jama'a.

Hakazalika muna ta jin tsirarrun wakokin yan gidan YNS musamman ma na Dj Ab da Teeswag domin sunata yaduwa a ko ina.

Don haka muke tambaya, shin wai ko kowa dake YNS ya kama gaban sa ne da yin waka shi kadai ko masu basirar yin waka ke yi kawai?

ADVERTISEMENT

A wata hira da suka yi a shirin h hip hop na Arewa24 Yaran North Side sun bayyana cewa burin su shine su gan wakokin su ya yadu a ko wani kasa dake duniya kuma su bunkasa al'adar yan arewa ta hanyar wakokin su.

Idan gaba yashigo tsakanin su ta yaya zasu cinma burin su?

Muna alfahari dasu kuma bamu gaji da jin wakokin su shiyasa muke son bayanin ainihin dalilin da yasa tsirarru kawai ke yin waka a farfajiyar su.

A cikin wani waka da suka yi Likitre ya sako baiti mai cewa "mutane su taho da kofunan su domin su sha mamaki saboda ga YNS sun yunkuro mun zo mu basu mamaki".

A shirye muke domin ganin abun mamakin.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT