ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Muhammadu Buhari yayi ma Sanata jaje game da mutuwar matarsa

Shugaban yace hakika mutuwar uwa yana ma ginshikin gida barazana domin irin ayyukan da take yi ga iyalin ta

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma iyalin dan majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje bisa ga rasuwar uwargidan sa Hajiya Yelwa Goje.

A sakon ta'aziya da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar ranar Litinin, shugaba Buhari yace mutuwar hajiya Yelwa ya razanar dashi.

Shugaban yace hakika mutuwar uwa yana ma ginshikin gida barazana domin irin ayyukan da take yi ga iyalin ta wajen kula da yara da kuma faranta ran su.

Daga karse shugaban ya ma Sanata Goje da iyalen shi addu'a na Allah ya basu hakurin jure wannan babban reshi kuma Allah ya jikan ta da Rahama.

ADVERTISEMENT

Hajiya Yelwa Goje ta rasu a asibiti dake ƙasar Amurka bayan wata ciwo da take fama da ita.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT