ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna yace an koma harkar noma ba bata lokaci

Gwamna Yari ya tabbatar cewa gwamnatin shi zata cigaba da biyan albashi ba bata lokaci kuma zata taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

Alhaji Abdulaziz Yari, Zamfara state Governor

Gwamna Abdulazeez  Yari ya bayyana cewa an cigaba da harkan noma a jihar Zamfara don gwamnatin jihar ta bada himma wajen samun sulhu tsakanin manoma da makiyaya da yan fashi.

Yayi wannan sanarwa a jawabin sa na bikin sallah a jihar Zamfara.

Yace, manoma da makiyaya sun cigaba da harkan su ba tare da wata matsala ba.

Yace kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa wajen neman sulhu wanda mataimakin sa Malam Ibrahim Wakkala,ke jagoranta ta karfafa wajen neman sulhu da zama lafiya.

ADVERTISEMENT

Gwamnan yayi kira ga al’ummar jihar da su zauna lafiya kuma su san cewa gwamnatin zata cigaba da taimakawa wajen tallafawa da  bunƙasa al’ummar jihar.

Ya yaba ma malamai dake jihar don wa’azuzuka da suka yi na zaman lafiya a cikin watan Ramadan. Yayi kira ga al’ummar da suyi amfanin da muhimmancin  watan Ramadan wajen tafiyar da alamuran su.

Gwamna ya tabbata ma al’umma cewa gwamantin shi zasu cigaba da biyan albashin ma’aikata cikin lokaci.

ƙungiyar yan jarida na NAN su ruwaito cewa gwamnan ya bikin sallah a garin shi dake karamar hukumar Talatan mafara inda ya ziyarci ayyukan da gwamnatin gudanarwa.

Yari ya kara da karban baƙoncin marayu 340 a gidan shi wajen yin bikin sallah

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT