ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan Shi'a da yan sanda sun sake gwabzawa, mutum daya ya rasu

Mabiyan sun taru ne domin gudanar da zanga-zangar kin jini game da cigaba da tsaran jagoran su, Ibrahim Elzakzaky wanda kusan shekara biyu kenan da kama shi

A labarin da jaridar The cable ta fitar, an harbi daya daga cikin yan shi'a dake shirin gudanar da gangami a yankin Maitama na birnin tarayya.

Mabiyan sun taru ne domin gudanar da zanga-zangar kin jini game da cigaba da tsaran jagoran su, Ibrahim Elzakzaky wanda kusan shekara biyu kenan da kama shi.

Bayan harbin barkonon tsohuwa da jami'an tsaro suka yi, sun kuma harbi daya daga cikin yan zanga-zanga yayin da gangamin nasu yayi tsanani.

Wannan ya biyo bayan sati daya da arangama da ya faru tsakanin mabiyan da jami'an tsaro a dai dai unity fountain dake nan Abuja wanda ya tayar da kura tare da razanar da al'umar garin.

ADVERTISEMENT

Yan shia dai suna gangami domin a saki shugaban su wanda jami'an yan sandan farar hula ke cigaba da tsaron duk da damar da kotu ta bayar na a sake shi.

An kama shi bisa bayan mummunar arangama da ya faru tsakanin mabiyan shi da tawagar hafsan sojojin Nijeriya Tukur Buratai.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT