ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan sanda sun gano makamai 198 a jihar Katsina

Kwamishnan yan sanda na jihar Muhamed Wakili ya sanar da haka yayin da ya zanta da manema labarai ranar laraba 28 ga watan Maris

Kwamishnan yan sanda na jihar Muhamed Wakili ya sanar da haka yayin da ya zanta da manema labarai ranar laraba 28 ga watan maris.

Kwamishnan yace hakan ta faru ne sakamakon umarnin da sufeton yan sanda na kasa ya bada ga kowani kwamishna da mataimakin sufeton yan sanda na yankunan dake fuskantar barazanar yan fashi.

Yace mafi yawanci, an gano makaman ne daga hannun barayin shanu da sauran yan fashi da makami dake safara a jihar.

Cikin makamai da suka gano akwai bindiga kirar AK-47 guda 20 bindigar da pistol 10,Dogayen bindigogi kirar G3l da SMG guda hudu.

ADVERTISEMENT

Sauran sun hada da bindigogin kirar irin ta gargajiya, albarusai da kunshin harsashi.

Daga karshe kwamishnan yayi jaddada cewa hukumar zata cigaba da kokarin da tak wajen kwato makamai daga hannun masu mallakar shi ba ta hanyar doka ba.

Ya kuma kira ga masu rike dasu da suyi gaggawa su mika su tun kafin lokaci ya kure masu.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT