Sanata Mathew Uroghide, ya shigar da karar a zaman majlisa da aka yi ranar alhamis 26 ga wata. Ya bukaci shugaban majalisa, Bukola Saraki, da ya amince ayi amfani da sashi 143 na kundin tsarin doka wajen cigaba da wannan yunkurin.
Yan majalisa na neman tsige shugaban kasa
Yace shugaban ya sabawa sashi 80 na kundin, wanda ke bayyana cewa duk wani kashe kudi da gwamnati zata yi, sai ta samu amincewar majalisa kafin hakan ya faru
Yace shugaban ya sabawa sashi 80 na kundin, wanda ke bayyana cewa duk wani kashe kudi da gwamnati zata yi, sai ta samu amincewar majalisa kafin hakan ya faru.
Shima dai, sanata Chukwuka Utazi ya goyi bayan yunkuri inda ya kara da cewa, likaci yayi da majalisar zata zarce hukunci kan lamarin.
Sai dai, sanata Abu Ibrahim yayi ikari cewa yunkurin da abokan aikin sa suka shigar, makirci ne daga jam'iyar adawa na watsa ma nagartar shugaban kasa a ido.
Dan majalisar mai wakiltar jihar Katsina, ya shaida cewa indai kan batun ne, a shirye suka su kaddamar da shaida kan matakin da shugaban ya dauka
Kan batun, shima sanata Shehu Sani ya nuna facin ran sa kan matakin da shugaban ya dauka, ya kira lamarin a matsayin cin fuska ga kundin tsarin kasa.
Shi dai, bai goyi bayan yunkurin tsige shugaban kasa amma, yayi kira na a mayar da kudin asusun kana a fara cinikin kamar yadda doka ta kafa.
A ranar laraba ne, shugaban majalisar, ya karanta wasikar da shuagan kasa ya tura masa mai, dauke da labari cewa, an cire kudin ne domin siyan wasu jiragen yaki ba tare da sanar da majalisa ba domin ta cinma tsarin da aka kafa kan kwantiragin.
Kamar yadda sakon ya bayyana, an tura kudin ne kai tsaye zuwa asusu gwamnatin kasar Amurka.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng