ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan bindiga sun kai hari kauyen Bakin kogi, mutum 6 sun mutu

maharan sun sanya rugunar sojoji da na ya sanda yayin da suka kai harin wanda yayi sanadiyar raunata wasu mutane hudu

Wasu yan bindiga sun kai hariin kauyen Bakin kogi na karamar hukumar Jama'a na jihar Kaduna inda suka kashe mutum 6 tare da raunata wasu 4.

A bisa rahoton da jaridar Guardian ta fitar, yan bindigar wadanda ake zargi cewa makiyaya ne sun kai harin ne sau biyu. harin na farko ya faru ne a dai dai karfe 10 na safe kana na biyun ya  faru karfe 11 duk a ranar alhamis 29 ga wat.

Wani jami'in kwamitin tsaro na kauyen mai suna Auta Maurice ya shaida cewa, yan bindigar sun kashe mutum uku na farko a dajin kauyen kana sauran mutane uku da suka rasu sun gamu da ajalin su ne yayin da maharan suka far masu a tsauni inda suke aikin tonon ma'adanai.

Ya kuma bayyana cewa maharan sun sanya rugunar sojoji da na ya sanda yayin da suka kai harin wanda yayi sanadiyar raunata wasu mutane hudu daban.

ADVERTISEMENT

A bayanin sa, kakakin hukumar yan sanda na jihar ASP Aliyu Mukhtar ya sanar cewa biyu daga cikin mamacin mata kana sauran hudu na maza ne.

Yace jami'an hukumar tare da hadin gwiwar sojoji suna cigaba da bincike wajen kama wadanda suka aikata mummunar laifin.

Harin dai ya faru rana daya da dakarun sojojin jihar suka binne wasu jami'an su 11 da wasu yan bindiga-dadi suka kashe a kauyen kamfanin Doka dake karamar hukumar birnin gwari na jihar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT